Kwamitin mutane 13 da ofishin mai ba shugaban kasa shawara akan tsaro ya kafa akan binciken kudaden da aka da kuma rashin sayen makamai da kayan tsaro a mika rahotan shi.
Shugaba Muhammadu Buhari
Bayan mika rahotan nasu, Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurni akan a kama tsohon mai ba shugaban kasa shawara kanar Sambo dasuki.
Kwamitin wanda aka kafa a ranar 31 ga watan Oktoba, har yanzu bai gama binciken shi ba. Amma dai ya gano wadannan abubuwan;
Sun gama bincike akan kudaden da aka kashe sojin kasa, na sama dana ruwa a kudaden kasa dana waje. An gano kudaden da aka kashe ma DSS da yan sanda banda kudaden da gwamnatocin jihohi suke basu.
An gano cewa an kashe sama da Dala Biliyan 1 akan aiyukan da ba’a ma yisu ba. Da kuma kudaden da aka ciyo bashin su a majalisar kasa
Sanna an gano cewa Dasuki ya bawa wani Kamfani Naira Biliyan 3 ba tare da an gano abunda ya sanya a basu ba.
Sannan an gano cewa daga shekara ta 2012-2015, Dasuki ya bada umurnin kashe Naira Bilyan 2, Dala Biliyan 1, da kuma Euro Miliyan 9 domina sawo jirgi mai saukar Angulu da makamai.
Rashin makamai dai shine korafin da sojojin Najeriya keyi akan tsaikon da suke samo wajen yakar yan Boko Haram. Wannan ne ya jawo mutanen dubunnan mutane a Arewa maso gabas.
Bayan mika rahoton nasu, shugaba Buhari ya bada umurni a kama Dasuki

0 comments:
Post a Comment