Sojojin Najeriya Sun Ba Masu Zanga Zangar Biafra Gargadi

Hukumar soji ta ba masu zanga zangar kada kasar Biafra gargadi cewa baza su tsaya ba su bar Najeriya ta shiga rudani saboda suna so su kafar kasar Biafra ta hanyar zanga zanga.
Zanga zangar Biafra
Tun farkon wannan watan dai masu zanga zangar ke ta yin zanga zanga a karkashin kungiyar MASSOB da kuma IPOB bayan da aka kama Nnamdi Kanu, shugaban rediyon Biafra.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Birigediya Janar Ibrahim Attahiru wada shine mukaddashin Kwamandan Barikin ta 82 dake a jihar Enugu ne ya bada wannan gargadi. Yace: “Muna so mu fada masu cewa ya isa haka nan.”
Ya bayyana cewa da zarar soji suka shiga cikin kawo karshen zanga zangar, zasu yi amfani da duka dokokin da suka dace. Ya kuma bayyana cewa basu shiga cikin hana aukuwar abun bane saboda yan sanda na yin bakin kokmarin su. Sanan ya bayana cewa Yan Sanda akwai iyakar abunda zasu iya yi.
Ya sannan kuma bayyana cewa wasu masu zasnga zangar sun yi barna da kone kone a Abakaliki, Enugu, Fatakwal da wasu jihohi.
Share on Google Plus

About Unknown

This is a short description in the author block about the author. You edit it by entering text in the "Biographical Info" field in the user admin panel.
    Blogger Comment
    Facebook Comment

0 comments:

Post a Comment