Masu zanga zangar Biafra sun kona wani masallaci a Onitsha, jihar Anambara a jiya Laraba 2 ga watan Disamba.
Arinze Esomnofu, mai rubutu ga Naij.com ta bayyana duka abubuwan da suka faru inda hake can yana kawo rahotanni.
Wata Mai goyon bayan zanga zangar ta rasa ranta bayan da wani jami’in
sojin ruwa ya -halbe ta bindiga. Suna wadda ta rasa ran nata Nkiruka
Anthonia Ikeanyionwu. Shekarun ta 21 kuma daliba ce a kwalajin ilimi ta
tarayya dake Umunze daga Adazi Nnukwu, daga JIhar Anambara.
Masu zanga zangar Biafra sun shigo gari sun ihu cewa a saki Nnamdi Kanu ko su duka su mutu. Sai suka tafi suka fara kona-Kone.
Masu bada shaida sun nuna cewa massallacin a Onitsha ne ke ci da
wuta. Wani Mai amfani da shafuka sada zumunta ya aiki da wasu hotuna
inda ya bayyana cewa MASSOB/IPOB ne suka sanya mashi wuta.
A Wata fira da Alphonsus Ikechukwu, jami’i mai hudda da jama’a ma
hukumar yan sandan jihar yayi da SaharaReporters, ya bayyana cewa masu
zanga zangar ne suka kona masallacin. Sannan kuma suka kona motocin
Dangote guda 6. Ya bayyana cewa suna damun al’ummar jihar kuma suna
kona-Kone.
Arangamar da akayi ta bar mutane 9 a mace, 5 daga gadar Nija, 3 daga
hanyar Obodoukwu, sai kuma wani mai saida suya wanda harsashi ne ya
kauce ya same shi. Jaridar Vanguard ta ruwaito.
Alphonsus kuma ya bayyana cewa yan sanda 2 sun rasa rayukan su sakamakon arangamar da akayi.
- Blogger Comment
- Facebook Comment
Subscribe to:
Post Comments
(
Atom
)
0 comments:
Post a Comment